1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

ICC za ta kama tsohon shugaban 'yan sandan Philippines Rosa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 11, 2026

A watan Maris na 2025 'yan sandan Philippines bisa hadin kan interpol suka kama tsohon shugaban kasar Rodrigo Duterte.

Tsohon shugaban Philippines Rodrigo Duterte tare da tsohon shugaban 'yan sandan kasar Ronald "Bato" Dela Rosa.
Tsohon shugaban Philippines Rodrigo Duterte tare da tsohon shugaban 'yan sandan kasar Ronald "Bato" Dela Rosa.Hoto: Bullit Marquez/AP Photo/picture alliance

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC da ke birnin The Hague, ta ba da umarnin kama tsohon shugaban 'yan sandan Philippines, kuma 'dan majalisar dattijai a yanzu, Ronald Dela Rosa, bisa zargin kisan dubban jama'a.

Karin bayani:An tsige mataimakiyar shugaban Philippines Sara Duterte

ICC na kallon Dela Rosa, a matsayin kanwa uwar gami, wajen aiwatar da shirin da shugaba Rodrigo Duterte ya bijiro da shi, na yaki da safarar muggan kwayoyi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutanen da ba-su-ji-ba-ba-su-gani-ba.

Karin bayani: Za a fara shari'ar tsohon shugaban Philippines a kotun ICC

A watan Maris na 2025 'yan sandan Philippines, bisa hadin gwiwar na kasa-da-kasa interpol, suka kama tsohon shugaban kasar Rodrigo Duterte, sannan suka mika shi hannun kotun ICC, kan zargin kashe mutane 6,252, daga ranar daya ga watan Yulin 2016, zuwa 31 ga Mayun 2022, da sunan yaki da miyagun kwayoyi a kasar.