SiyasaAfirka
ICG: Babu alamun Boko Haram ta fara saduda
July 7, 2020Talla
A cikin wani sabon rahoto da kungiyar International Crisis Group ta fitar a wannan Talata ta ce mayakan jihadi sun yi nasarar sake farfadowa a sakamakon yadda kasashen yankin suka gaza samar wa rundunar tsaron MNJTF din kudi da kayan aiki. Kungiyar ta ce a bisa binciken da ta gudanar babu wata alama da ke nuna cewa mayakan Boko Haram sun fara saduda.
Tun a shekara ta 2014 ne dai kasashen Kamaru da Chadi da Nijar gami da Najeriya suka suka kafa wannan runduna domin magance hare-haren Boko Haram, sai dai acewar International Crisis Group gwamnatocin wadannan kasashen na bukatar yi wa rundunar garambawul ta hanyar gyara tsarin tattara bayanan sirri da magance cin zarafin mutane da ake zargin rundunar da shi.