ICJ ta yi watsi da bukatar karin kariya ga Falasdinawa
February 17, 2024Talla
A watan Janairun da ya gabata ne kotun ICJta umurci Isra'ila kan ta dauki dukkanin wasu matakan da zai hana dakarunta aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa a Zirin Gaza, karar da kasar Afirka ta Kudu ta shigar.
Karin bayani: Kotun MDD zata fara shari'ar Pretoria da Isra'ila kan Gaza
Sai dai a ranar Talatar da ta gabata, kasar Afirka ta Kudun ta sake shigar da karin koke na neman daukar sabin matakan dakile shirin Isra'ila a Rafah. Kotun ta ce hare-haren na kara jefa yankin cikin bala'i da dama yaki ya daidaita, sai dai bata bayyana wasu matakai da za a dauka ba. Hukuncin da aka yanke ya kuma nuna cewa Isra'ila har yanzu bata kammala sauke nauyin da ke kanta ba karkashin dokar hana kisan kare dangi.