Siriya: 'Yan tawaye sun ki amincewa da sulhu
September 23, 2018![Türkei beginnt Offensive Operation Afrin in Syrien](https://static.dw.com/image/42238570_800.webp)
Talla
Kasashen na Rasha da Turkiyya sun shawarci yan ta'addan da su kauracewa yankin da sojojin kasashen biyu suka yi sansani kafin ranar 10 ga watan Oktoba mai kamawa, a cigaba da yunkurin kawo karshen yakin kasar.
Da suke mayar da martani cikin wata sanarwa. 'yan tawayen sun umarci mayakan kungiyar da su cigaba da kai hare-hare. Akalla fararen hula miliyan uku ne ke zaune a yankin na Idlib kafin yakin da ake gwabzawa a kasar ya mayar da su 'yan gudun hijira.