Igiyar ruwa ta koro gawarwakin 'yan cirani
December 27, 2021![Europa | Seenotrettung im Mittelmeer](https://static.dw.com/image/57518493_800.webp)
Rahotanni daga kasar ta Libiya sun nunar da yadda igiyar ruwa ta koro gawarwakin 'yan cirani 28 gabar tekun kasar, bayan nutsewar kwale-kwalensu a yayin da suka yi kokarin bin barauniyar hanya don shiga nahiyar Turai a karshen makon da ya gabata. Rahotan ya kara da cewa, an dauki kwanaki da samun nutsewar kwale-kwalen gabanin samun gawarwakin a gabar ruwan mai tazarar kilomita casa'in daga birnin Tripoli.
Mashigin ruwan Libiya a baya-bayan nan, ya kasance a matsayin babbar hanyar da ‘yan cirani ke amfani da ita don tsallakawa Turai duk da yadda suke rasa rayukansu a kowacce rana. Wannan Ibtila’in na zuwa ne kwanaki kalilan bayan mutuwar ‘yan cirani 160 a dai hanyar ta Libiya cikin kasa da mako guda wanda ya mayar da adadin rayukan da aka rasa cikin shekarar nan zuwa mutum dubudaya da dari biyar.