1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Bala'i

Igiyar ruwan tsunami a New Caledonia

Gazali Abdou Tasawa
December 5, 2018

Gwamnatin New Caledonia ta gargadi al'ummarta da ta dauki matakan buya a sakamakon igiyar ruwan tsunamin da aka hango a tsakiyar ruwan yankin biyo bayan wata girgizar kasa.

Chila - Schäden nach Erdbeben
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Hernandez

Gwamnatin kasar New Caledonia ta gargadi al'ummar tsibirin na yankin Tekum Pacifik da ta dauki matakan buya a sakamakon igiyar ruwan tsunamin da aka hango a tsakiyar ruwan yankin biyo bayan wata girgizar kasa mai karfin murabbadi 7,5 a ma'aunin girgizar kasa na Richter da ta wakana a wannan Laraba a wani waje mai nisan kilomita 300 da babban birnin kasar na Noumea.

 Mahukuntan kasar dai sun aika da sakonni kar-ta-kwana ga al'ummomin kasar suna masu gargadinsu da su dauki matakan buya domin kauce wa fadawa tarkon igiyar ruwan tsunamin mai tsawon sama da mita uku da aka hango ta taso ta kuma tunkaro gabobin ruwan kasar ta New Caledonia da Vanuatu a yayin da wata igiyar tsunamin mai tsawon mita daya ta tunkari Tsibirran Fidji. 

Kasar New Zeland ma ta tayar da jiniyoyin gargadin jama'a kan barazanar igiyar ruwan tsunamin kafin daga bisani ta dakatar da su. Kawo yanzu dai babu wani bayani a game da barnar da yankin ya fuskanta bayan afkuwar girgizar kasar.