1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Yunkurin kare muhalli daga kamfanonin duniya

Usman Shehu Usman
October 29, 2021

A daidai lokacin da ake taro kan sauyin yanayi na duniya, masana na cewa da wuya a samu kamfanin da baya ambaton kare mahalli, ko da kuwa yana cikin masu gurbata shi.

Nigeria Tschadsee-Region Fluten
Hoto: DW/A. A. S. Muhammad

Ga misali babban kamfanin dake da shagunan sayar da kayan abinci kamar Aldi da kuma REWE sun yi alkawarin amfani da kayaki mara gurbata mahalli kwata-kwata nan da shekaru 18, a ya yinda kamfanin sarrafa siminti na kasar Jamus wato HeidelbergCement, yace shi kuwa nan da shekaru 30 yanan saran yin amfani da kayaki marar gurbata mahalli. Sabine Nallinge, ita ce shugabar ZweiGrad wata gidauniyar yaki da gurbacewar mahalli, yana cewa. "Kamfanonin tattalin arziki sun fara gane cewa yanzu dukkan duniya ta maida hankali wajen kaucewa sauyin yanayi. Don haka kamfanin ke son zama a suhun gaba, bawai su zauna a nuna masu yadda ake aiwatar da tsarin kare mahalli ba."

Karin Bayani: Barazanar yunwa a kasashen duniya

Hoto: Charlie Riedel/AP/picture alliance

Gaba daya dai yanzu haka a fadin duniya kamfanoni kimanin 500 suka sanar ware dala bilayan daya don kula da sauyin yanayi, kuma a yanzu kusan kowane mako ana samun cigaba daga bangaren kamfanoni da ke da wannan ra'ayi, a wani binciken da cibiyar Wuppertal mai kare mahalli ta gudanar. Don haka cewar masaniyar babban dalilin shi ne yawaitar fadakarwa da 'yan fafitika suka yi a tsakanin al'umma. "Hankan ya hadu da yadda jama'a ke mahawara bisa illar gurbacewar mahalli, da kuma kungiyoyi kamarsu Fridays for Future. Hatta su kansu masu ra'ayin kin harkar yaki da muhalli a baya, yanzu suna jin ana fadawa yara illar da cin biredi da sauran kayakin amfanin yauda kullum da ke gurbata mahalli. Kuma matasan sun fara gane cewa iyayensu ma na da hannu a gurbata mahalli."

Karin Bayani:IPCC: Bukatar matakin gaggawa kan yanayi

Hoto: Azwar Ipank/AFP

Sai dai fa duk wannan ikirarin da kamfanoni da gwamnatoci ke yi na kare mahalli, akwai wata babbar ayar tamba ta sahihancin abin da suke fada, domin waye ke sa'ido bisa yadda suke aiwatar da kare mahallin kamar yadda suke fada, yaya gaskiyar aikin ke gudana. Akwai matukar karancin masu sa ido na aiwatar da ikirarin da ake yi. Nicolas Kreibich masani ne a cibiyar ta Wuppertal "Matsayin na magance sauyin yanayi, a yanzu ya doshi wani lokacin da ba wanda ake iya matsawa ya yi hakan, tunda ko ya amince yana yaki da gurta mahalli, wannan kuma shi ne hatsarin da ake gudu."

Kamfanoni da yawa a yanzu suna ta shiga sahun masu yaki da sauyin yanan yi bawai bisa son ransu ba, amma har ta kai anan shigar da su kara a kotuna don kasancewarsu na masu gurbata mahalli wanda ke zama illa ga duniya, don haka yanzu ko wane kamfani ke son cewa shi ne a gaba a yaki da gurta mahalli yadda za basu takardun shaidar cewa sufa masu cikakken aiki ko saffara kayakin da suka dace da mahlli.