Ikrarin lashe zaben Tunusiya
September 16, 2019'Yan takarar biyu na wato Nabil Karoui hamshakin attajirin nan da ke tsare a gidan kaso bisa zargin tsarkake kudaden haram da kuma Kais Saied dan takara mai zaman kansa, sune suka yi ikrarin kasancewa a sahun gaban, a zaben shugaban kasar da ya gudana a karshen mako.
Wasu cibiyoyin kididdigar sakamakon zabe masu zaman kansu, sun bayyana cewa Kais Saied na a kan gaba da kaso 19 daga cikin dari a yayin da Nabil Karoui ya samu kaso 15 daga cikin 100 na kuri'un da aka kada, wanda ke nufin cewa sune za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.
Idan dai har hukumar zaben kasar ta ISIE ta tabbatar da wadannan alkalumma a hakumance a gobe Talata, to kuwa hakan zai zamo wani babban ruguntsumi a fagen siyasar kasar ta Tunusiya, kasancewar babu daya daga cikin shugabannin siyasar kasar na bayan juyin-juya hali na 2011, da ya yi nasarar ketarawa zuwa zagaye na biyu na zaben wanda ya hada 'yan takara 26.