Illar bunkasar kasuwancin gawayi a Najeriya
November 28, 2017Sai dai kuma masana muhalli su na gargadin irin matsalar da ka iya faruwa sakamakon yadda ake sare itatuwa da sunan samar da gawayin.
Sakamakon yadda farashin kananzir wadda mafi akasarin al'ummar Najeriya masu karamin karfi suka fi amfani da shi wajen makamashi, ya sanya jama'a suka karkatar da hankalinsu ga amfani da gawayi domin amfanin yau da kullum kamar girki da sauran su. Garin Nabordo dake karamar hukumar Toro na daga cikin inda harakar gawayin ta yi nisa. Abubakar Othman daya ne daga cikin masu harkar kona gawayin.
Haka zalika a cikin birnin Bauchin ma dai gawayin ya samu karbuwa saboda halin tsadar rayuwa da jama'a ta ke fama da shi, inda kusan dukkan manyan hanyoyi da lungu da sako ake samun masu sayar da shi.
Yanzu haka dai harkar gawayin dai bata tsaya a iya cikin Najeriya ba, inda a kan fitar zuwa kasashen Turai da Asiya musamman ma kasar China wadda a cikin watan Nuwambar wannan shekara ta kulla alakar cinikayya mai karfi da jihar Bauchi kan gawayin.