Bukatar inganta tsabtar muhalli
November 19, 2015Talla
Ban ya ce wannan batu dai shi ne na rashin tsabtar muhalli da kuma samun abinci mai tsabta. Ban ya bayyana hakan ne a wannan Alhamis, a yayin bikin tunawa da ranar bandaki ta duniya da aka saba gudanarwa a ranakun 19 ga watan Nuwamba na ko wacce shekar. A kiyasin Majalisar Dinkin Duniya dai sama da mutane biliyan biyu na zaune ne a muhallin da ba shi da tsabta, yayin da kusan biliyan guda ba su da bandaki a duniya suna yin bahaya ne a wuri budadde. Ban ya kara da cewa rashin tsabtar muhalli na daya daga cikin muradun ci gaban karni na majalisar wanda ya zo karshe a wannan shekara da muke ciki da al'ummomin kasa da kasa suka gaza cimma.