Illoli da ke tattare da leda a muhalli
July 31, 2016Daga cikin manyan illolinta shi ne ba ta narkewa ta kan dauki sama da shekaru dari ba ta narke ba a cikin karkashin kasa, kuma idan ma ta narke sinadaranta na da illa ga dan Adam. Ita tana illa a ayyukan gona ko gini misali idan ta na karkashin kasa ba ta bari ruwa ya ratsa kasa. Sannan manoma ko makiyaya idan dabbobinsu suka ci tana halaka su.
Leda abin da kowa yake gani shi ne yadda take rufe magudanan ruwa kamar misali a Malesiya shekara da shekaru suna fama da matsalar ambaliyar ruwa, hakan kuma na faruwa ne saboda leda, dan haka sai aka yi taron masana muhalli bayan da suka fitar da rahoto aka yi amfani da shi an samu sauki da kashi hamsin cikin dari.
Idan leda ta yi yawa a muhalli ko kyan gani baya yi, sannan idan da a ce za ta narke idan aka yi noma a inda take mutane suka ci abincin zai musu illa.
Tsarin mahukunta
Da yawa mahukunta a kasashenmu na Afirka ba sa ba wa tsarin kula da muhalli muhimmanci saboda idan a ce akwai tsari kamar a kasashe da suka ci gaba inda za ka ga tsarin kula da shara na musamman ne, to da an samu ci gaba. Su kansu al'umma sai sun zama masu bin doka da oda sai kaga mutum dan Boko amma yana tafe yana zubar da shara wanda kuma bai karatu ba yana bi ya share ai wannan abin kunya ne.
Mafita
Na farko a fitar da tsare-tsare masu muhimmanci ga muhalli mutane da ba sa bin doka a hukuntasu , sannan a nema wa al'umma makamanciyar ledar misali a Japan ledar da ake amfani da ita an hada ta da wasu sinadare da ke da wa'adi da za a iya amfanarta muddin wa'adin ya cika za ta wargaje ne ta bi isaka kawai.
Ana iya sanya haraji a ledar zai sa al'umma su rage amfani da ita, dan sai ka sa kudi za ka siya sannan ba za ka jefar da ita ba ko'ina ba, kana iya kara amfani da ita. Kudin da aka samu ta siyar da ita ana iya amfani da su a alkinta muhalli.