Taro kan sauyin yanayi: Akwai alfanu?
June 27, 2019Talla
Matsalar sauyi ko dumamar yanayi, matasala ce da tuni ta zama ruwan dare gama duniya. Illolin sauyi ko dumamar yanayi sun hadar da kwararowar hamada da fari da ambaliyar ruwa da tsananin zafi da sanyi. Kwararru da masu ruwa da tsaki kan yi tarurruka domin lalubo hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan matsala da ke kokarin zama ta gagari kundila.