1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta karrama wata 'yar asalin Afirka

October 20, 2020

Wata gidauniyar da ke karrama 'yan Afirka a Jamus ta zabi baiwa wata 'yar asalin kasar Somaliya lambar yabo ta wannan shekarar ta 2020 a birnin Berlin.

USA Ilwad Elman
Hoto: Getty Images for BET/E. Gibson

Nan gaba kadan ne a cikin wannan watan na Oktoban da muke ciki, cibiyar da ke bayar da lambar yabo ga 'yan Afirka mallakin gwamnatin Jamus zata karrama Ilwad Elman wata 'yar Canada da Somaliya.

Ministan harkokin wajen jamus Heiko Maas ya ce za a gudanar da bukin ne a Birni Berlin. Ilwad din da ke da tushe a kasar Somaliya ta kasance 'yar fafutuka kuma mai gudanarda ayyukan jin kai ga mata da yara kanana da aka tsunduma cikin ayyukan soji a lokacin yakin basasar kasar ta Somaliya.

Mai ayyukan na jin kai mai shekaru 30 da haihuwa, ta kasance macen da aka fi jin muryarta a kasar, wajen sauya tunanin yara bayan da ta fito da wani tsarin ilmantar da su mai taken ''A ajiye makami a dauki alkalimi'' wanda irin wannan tsari nata ke yin tasiri a kasashen Mali da Chadi, inda kuma ake sa ran jarraba shi a suran kasashe da ke fama da kalubalen tsaro.

Ilwad Elman da mahaifiyarta wadanda yaki ya tilasta masu yin gudun hijira zuwa Canada tun tana 'yar shekaru 2, inda suka koma mahaifar ta su a shekara ta 2010 domin cigaba da gudanar da ayyukan jin kan da mahaifita Elman Ali Ahmed ya bari, bayan da wasu da ba a san ko su wa nene ba suka hallaka shi.