Tattalin arzikiMexiko
IMF: Karin haraji zai dakushe tattalin arzikin duniya
April 22, 2025
Talla
Shugaban Amurka Donald Trump ya jefa tattalin arzikin duniya cikin halin koma baya wanda ya rage hasashen ci gaban tattalin arzikin duniya a 2024 da kashi 2.8% a cewar asusun bada lamunin na duniya IMF a rahoton da ya fitar.
An yi tsammanin tattalin arzikin zai tsaya a kashi 3.1% kamar yadda ya kasance a 2024 da ma yiwuwar bunkasa zuwa kashi 3.3% a 2025 a cewar mai bayar da shawara ga asusun na IMF kan tattalin arziki Pierre-Olivie Gourinchas. Asusun ya ce sanarwar Trump kan karin haraji a watan Afrilu ya kawo tsaiko ga tattalin arzikin duniya.
Gourinchas ya ce matakin ramuwar gayya da China ta dauka kan Amurka ya rage dangantakar cinikayya a tsakanin kasashen wanda ya kuma ya yi tasiri a kan ci gaban kasuwanci a duniya.