1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe masu tasowa sun sami rancen IMF

April 15, 2020

Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF, ya bayar da rancen gaggawa ga wasu kasashe masu tasowa tare da yafe wasu daga cikin basussukan da asusun ke bin au, domin su samu karfin gwiwar fuskantar matsalar annobar Coronavirus.

IWF Direktorin Kristalina Georgieva
Shugabar Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF Kristalina GeorgievaHoto: Imago Images/Xinhua/Liu Jie

Asusun yayi amfani da kudi da ya ware na bayar da dauki idan bala'i ya auku a cikin kasashe. Sai dai masana tattalin arziki da masu sharhi na aza tambaya a kan tallafin da kasahen za su ranta. A cikin wani jawabi da ta yi a ranar Litinin din da ta gabata, a yayin bikin Easter, shugabar asusun Kristalina Georgieva ta ce asusun na IMF zai ci gaba da bayar da tallafi wajen yaki da annobar ta Coronavirus da kuma na irin koma bayan tattalin arzikin da annobar za ta janyowa kasahen.

Yafe basussuka

Kasahe 25 Asusun ba da Lamunin na Duniya IMF ya afewa basussukan a karkashin tsarinsa na yin sassaucin basukan, tare da bayar da tallafi ta hanyar asusun CCRT. Asusun na CCRT an kafashi ne a shekara ta 2015 a lokacin da annobar Ebola ta barke, inda ake amfani da shi wajen bayar da tallafi ga kasahen da suka fuskanci bala'i. Jürgen Kaiser da ke zaman wani masanin harkokin siyasa da tattalin arziki na cibiyar ERSSAJAHR ya ce wanan labari ne mai dadi.

Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF zai bayar da rancen gaggawa ga kasashe masu tasowaHoto: Reuters/Y. Gripas

Daman dai Asusun ba da Lamunin na Duniya IMF, irin tsarin da ya yi amfani da shi ke nan a shekara ta 2000, domin kaddamar da shirin PPTE na ba da tallafi ga kasahen da ba su ci-gaba ba, wadanda talauci ya yi wa katutu, bayan kammala taron kasahe masu karfin tattalin arziki a duniya  G8 a shekara ta 1999, inda asusun ya yafewa kasahe 36 matalauta wadanda bashi ya yi wa kanta basusuka.

Tattalin arziki ya girgiza

Daga cikin kasahen da suka ci moriyar wannan tallafin na Coronavirus da za a bayar rance har da Senegal da za a bai wa miliyan 442 na dala Ghana kuma za ta samu biliyan daya sannan asusun ya sha alwashin tallafa wa wasu karin kasashe 76. Annobar dai ta Coronavirus wacce ta bazu a cikin kasahen duniya, ta kassara tattalin arzikin kasahen wanda za a dade ba su samu irin yadda suke so ba.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani