IMF ta nemi karin tallafi ga Girka
November 15, 2012Talla
Hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF, a wannan Alhamis ta nemi ƙasashen Turai su saka hannu wajen rage bashin ƙasar Girka, inda hukumar ta ce, ta daina bada gudumawar ceto tattalin arzikin ƙasar ta Girka.
Hukumar ta ƙara lokacin da Girka za ta biya bashi zuwa shekaru huɗu. Amma hukumar ta IMF, ba ta bayyana dalla-dalla yadda ta ke bukatar ƙasashen za su tallafa wa Girka ba.
Shugaban hukumar ta IMF, Christine Lagarde za ta katse ziyarar kasashen Asiya, domin halartar taron ministocin kudin kasashen masu amfani da kudin Euro, bisa ruikicin na kasar ta Girka, ranar Talata mai zuwa.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasir Awal