1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar

Zainab Mohammed Abubakar
September 9, 2020

Shugabar Asusun bada lamuni ta duniya, watau IMF Kristalina Georgieva ta ayyana alamun sake farfadowar tattalin arzikin duniya da ya durkushe sakamakon annobar corona.

Belgien EU Irak Kristalina Georgieva EU-Kommissarin für Katastrophen und humanitäre Hilfe
Hoto: picture-alliance/dpa

Amma murna na iya komawa ciki idan har ba a yi nasarar samun allurar riga kafin cutar ta COVID 19 ba.

A wani sharhin da ta yi hadin gwiwar rubutawa da babbar jami'ar tattali ta asusun na IMF Gita Gopinath, jami'an sun jaddada muhimmancin gwamnatoci su cigaba da taimakawa ma'aikata da 'yan kasuwa, kasancewar halin da ake ciki ya janyo mutane da yawa sun rasa ayyukansu, daura da karayar arziki.

A daidai lokacin da kasashen duniya ke sassauta dokar kulle da takaita zirga zirga, harkokin kasuwanci da ma ayyuka sun fara farfadowa, batu da ke nuna yiwuwar shawo kan matsalolin tattalin da annobar corona ta haifar.