1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin 'yan IPOB da jami'an tsaro

Muhammad Bello
April 26, 2021

Jami'an tsaro na ci gaba da dauki ba dadi da 'yan bindigar da ake zargin 'yan rajin Biafra ne a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya da wasu sassan yankin.

Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

A baya-bayannan dai, bayan 'yan bindigar sun kai hari gidan gwamnan Jahar Imo da ke kauyensu, haka kuma sun kai hari gidan wani basaraken Anambra, da kuma kan wasu jami'an tsaro a jihar Rivers, inda suka halaka da daman su.

Hare-haren baya-bayan nan din dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnonin yankin Kudu maso Gabashin na Najeriya, wato yankin da ya fi fuskantar hare-haren, suka kirawo wani taron gaggawa na tsaro a jiya a jihar Enugu a yankin.

Yankin na Kudu maso Gabashin na Najeriya dai, da a nan ne kabilar Igbo take, tuni ya sauya zuwa yanki na tashe-tashen hankula, inda ake zargin 'yan rajin Biafra bangaren IPOB da Nnamdi Kanu ke jagora da assasawa.

Hoto: DW/K. Gänsler

A 'yan watannin nan dai sun ta kai hare-hare kan barikokin 'yan sanda, da chek chek point na 'yan sandan, gami kuma da wadda suka kai kan hedikwatar rundunar 'yan sandan Imo a inda kwamishinanta yake, tare kuma da kai hari kan gidajen gyaran hali biyu, inda suka samu nasarar balle daya daga ciki tare da barin daurarru su tsere.

Ko da yake dai jami'an tsaro a yankin da garari ya kai garari, sun kai ga dena fita da kayan sarki, su na ci gaba da kokarin tunkarar 'yan bindigar, da har yanzu ke ci gaba da ta'annacin su a yankin.

Jihar Imo dai a yanzu, za a iya cewar ta fi fuskantar wannan balahirar ta 'yan bindiga da daukacin shugabannin yankin ba sa so ace 'yan rajin Biafra ne na IPOB, kuma daga bayanai, mazauna Jihar musamman 'yan ci rani, na ci gaba da zaman dardar.