1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaPakistan

An haramta wa Imran Khan shiga takara a Pakistan

Abdoulaye Mamane Amadou
December 30, 2023

Kwanaki bayan da wata kotun ta bayar da belinsa, hukumar zaben kasar Pakistan ta haramta wa tsohon firaministan kasar Imran Khan tsayawa takara a zabe

Imran Khan I Tsohon Firaminista a Pakistan
Imran Khan I Tsohon Firaminista a Pakistan Hoto: Mohsin Raza/REUTERS

Hukumar zaben Pakistan, ta yi watsi da takarar tsohon firaministan kasar Imran Khan, a babban zaben kasar da za a gudanar a shekarar 2024 mai zuwa.

A cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Asabar, hukumar ta ce ta yi watsi da takarar Imran Khan din ne, saboda hukuncin kotu da aka yanke masa a baya.

Hukumomi a kasar Pakistan na zargin tsohon firaministan ne da aikata laifin cin hanci, lamarin da ya janyo masa hukuncin daurin shekaru uku, sai dai a makon jiya kutu ta bayar da belinsa.