1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceGabas ta Tsakiya

Zirin Gaza: Mecece makomar al'umma?

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 24, 2025

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, ba za ta iya bayyana adadin motocin dakon kaya makure da kayan agajin jin-kai da ke jiran shiga yankin Zirin Gaza na Falasdinu ba

Falasdinu | Yunwa | Zirin Gaza | Kayan Agaji | Isra'ila | Yaki | Hamas
Hana shigar da kayan agaji, na barazana ga yankin Zirin GazaHoto: Dawoud Abu Alkas/REUTERS

Kakakin Hukumar Agajin Jin-kai ta Majalisar Dinkin Duniyar OCHA Jens Laerke ne ya shaidar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, inda ya ce duk da rokon da sukai ta yi mahukuntan Isra'ila sun yi kememe sun ki bayar da dama. Wannan na zuwa ne, a daidai lokacin da Tel Aviv ke ci gaba da fuskantar suka daga al'ummomin kasa da kasa saboda fargaba kan makomar al'ummar yankin na Zirin Gaza da yawansu ya kai sama da miliyan biyu da ke cikin halin taskun neman agajin jin-kai.

Sama da kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa 100 sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar a fuskanci matsananciyar yunwa a yankin, saboda hana kai kayan agajin jin-kan da sojojin Isra'ila ke ci gaba da yi. Koda a Larabar da ta gabata 23 ga watan Yulin 2025 ma, sojojin Isra'ilan sun hana bayar da damar shigar da kayan agaji cikin Falasdinu tare da yin ikirarin akwai kimanin motocin dakon kaya 950 da ke kan iyakar Gaza suna jiran a sauke kayan da ke cikinsu a raba su ga mabukata.