1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rivers: Ina makomar gwamna Fubara?

Muhammad Bello LMJ
May 21, 2026

Gwamnan jihar Rivers da ke Najeriya Siminalayi Fubara ya sanar da janyewarsa daga shiga zaben fitar da gwani, na dan takarar gwamna a jam'iyyarsa ta APC.

Najeriya | Rivers | Gwamna | Siminalayi Fubara | Takara
Gwamnan jihar Rivers Siminalayi FubaraHoto: Muhammad Bello

Ko da yake sanarwar ta zowa magoya bayansa da dama  da mamaki ana zargin Gwamna Siminalayi Fubara ya ci gaba da samun matsin lamba ta siyasa, inda har ma aka kai ga barazanar tsige shi daga kan kujerarsa. A iya cewa dambarwar siyasar Rivers tsakanin Gwamna Fubara da uban gidansa a siyasa Nyesom Wike a yanzu tazo karshe, ganin da ma matsayin da Wike ya dauka shi ne dole Fubara ya daina tunanin sake hawa kan kujerar gwamnan jihar a karo na biyu.

Wike  ya take farantin Fubara

Sanarwar ta Fubara da haka kwatsam ya janye daga takarar kujerar gwamnan jihar a karo na biyu, al'amari ne da wasu ke nuni da karfin iko na siyasar  Wike a Rivers din. Tun shekaru biyu baya ne Wike ya bayyana cewa, ya raba garin siyasa da Fubara illa kawai ko dai ya lallaba ya karasa wa'adinsa ko kuma a tsige shi. Salon takun siyasar ta Fubara musamman yadda ya ringa tunkarar rigimar da ya janyo da kansa, ya sanya magoya bayansa da masu sharhi siyasa ganin bai nuna kwazon siyasa ba.

Tshohon gwamnan jihar Rivers kana ministan Abuja Nyesom WikeHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP

Ayyana janye takarar tasa da ya yi a yanzu, ya sake hassala magoya bayansa da dama. Ko da yake Fubara ba dadewa ya yi wuf ya sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki ta APC daga PDP tare da nuna cikakkiyar mubaya'a ga shugaban kasa, hakan bai sa ya samu shiga a wajen Shugaban Bola Ahmed Tinubu da ma jam'iyyar ta APC a matakan jiha da kasa ba. Yadda jam'iyyar ta APC ke bai wa gwamnoninta damar shugabanci a jiha, Fubara din bai samu haka ba. Yadda aka yi fatali da 'yan takara da ke bangaransa ma, na nuna yadda saka kafar wando daya da ya yi da Wike din tun asubar fari ya janyo masa koma-baya a siyasa.

Barazanar tsigewa ta taka rawa

Barazana ta tsige shi daga kan kujerar sa a yanzu, na daya daga batun da aka tunkari Fubara da kuma ya sa ba shi da wani zabi face ya janye jiki daga wannan takara da ya sha bai wa magoya bayansa kwarin gwiwar da shi za a yi. A yanzu tuni magoya bayan Sim Fubara da dama, sun fara ruguguwar fadawa jam'iyyar NDC daga jamiyyar ta APC da Fubara ya kwashe su ya kai kuma ta sake su a igiyar ruwa. Makomar siyasar Fubara a jihar Rivers, ta zamo abin da ake ta tattaunawa a tsakankanin jama'a.

Gyarawa Wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW