Najeriya: Barazanar darewar jam'iyyar APC
May 8, 2025
Suna dai ta gudanar da taruka a daidai lokacin da guguwar sauya sheka da ma ficewa daga jamiyyun siyasun Najeriya ke ci gaba da tayar da kura a fagen siyasar Najeriya, tun kafin shekaru biyu da mulkin jamiyyar APC a kasar siyasar ta dau dumi. Ficewar da wasu 'yan jamiyyar ta APC mafi yawansu 'yan tsohuwar jam'iyyar CPC su ka yi, na daga hankula kan makomar jam'iyyar mai mulki duk da karbar sababbin magoya baya a yanayin na tsoron gangan in ta faye zaki ko za ta iya fashewa. Kusan dai dukkanin jiga-jigan da suka yi dalilin hadewar tsohuwar jam'iyyar ta CPC a 2013 da ACN a lokacin da aka samar da jam'iyyar ta APC ne, ke hallartar taron da shi ne irinsa na farko tun bayan hadewar da suka yi.
Shin tsorata suka yi da abin da ke faruwa a fagen siyasar Najeriyar, na kafa babbar jam'iyyar adawa a kasar domin tunkrar jam'iyyar APC a 2027? Tuni dai tafiya ta yi nisa, ga wadanda suka fice a karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufai da ma wasu 'yan jam'iyyar PDP. Akwai dai korafe-korafe, a kan yadda gwamnatin ke tafiyar da mulkinta daga sassan Najeriyar musamman yankin arewacin kasar. Harkokin siyasar Najeriyar na kara zafi sosai musamman yawan sauya sheka da ake yi da ya sanya tsohon shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan kashedin cewa, jam'iyya daya ba za ta yi wa dimukuradiyyar Najeriyar kyau ba.