1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka: Ko kasuwanci mara shinge zai yi wu?

Isaac Kaledzi LMJ
July 10, 2025

Har yanzu shirin samar da tsarin kasuwanci mara shinge a tsakanin kasashen Afirka, na zaman babban kalubale ga kungiyar Tarayyar Afirka.

Afirka | AU | Tarayyar Afirka | Mahmoud Ali Youssouf | Kasuwanci Mara Shinge
Shugaban Hukumar kungiyar Tarayyar Afirka AU Mahmoud Ali Youssouf.Hoto: BRYAN R. SMITH/AFP/Getty Images

Tsarin dai zai bayar da damar shige da fice a tsakanin kasashen na Afirka da ke cikin kungiyar Tarayyar Afirka ba tare da shinge ba, hakama zai bayar da damar yin kasuwanci a tsakaninsu ba tare da shingen ba. Sai dai har yanzu, kasashen Afirka da dama ba su yadda da fara aiwatar da tsarin ba. Kasashen Afirka hudu ne dai kawo yanzu wato Mali da Nijar da Ruwanda da kuma São Tomé and Príncipe, suka fara aiwatar da tsarin dokar zirga-zirgar jama'a da kayayyaki da ma fasaha ba tare da shinge ba na yarjejeniyar 2009.

Karin Bayani: Najeriya: Koma baya a cinikayya da Afirka

Kasashe 32 ne dai suka rattaba hannu kan shige da ficen haja a tsakaninsu, wanda kuma ake bukatar karin wasu kasashen akalla 15 kafin cimma mataki na gaba wajen fara aiki da daftarin dokar gadan-gadan. Yarjejeniyar ta bai wa kasashen Afirka damar gudanar da kasuwanci da zirga-zirga a kan iyakokin nahiyar ba tare da shinge ba, to sai dai babban kalubalen da shirin ke fuskanta shi ne rashin samun cikakken goyon baya da hadin kai daga gwamnatocin kasashen nahiyar.

Ko sai yaushe burin kungiyar Tarayyar Afirka na kasuwanci mara shinge zai cika?Hoto: S. Getu/DW

Galibin kasashen nahiyar Afirka na fargabar rasa kudin shiga da suke samu daga takardun izinin shiga kasa na Visa da batun tsaro da kuma aiwatar da dokokin kan iyakoki, a matsayin dalilan da ke haifar da tazgaro wajen aiwatar da kasuwancin na bai daya a tsakanin kasashen na Afirka. Wannan ya sanya kungiyar Tarayyar Afirka nuna damuwarta, kan yadda gwamnatocin kasashen nahiyar ke jan kafa wajen cimma muradun shirin. Masana dai sun yi ittifakin cewa batun tsaro da kuma fasakwabrin kayayyakin da aka haramta, ka iya kasancewa dalilan jan kafar.

Karin Bayani: Kasashen Afirka na kokarin fadada arzikinsu

Sanata a majalisar dattawan Kenya kuma mai rajin ci-gaban Afirka Margaret Kamar ta ce, baya ga batun tsaro akwai kuma bukatar samar da tsarin kula da kan iyakoki na bai daya. Gwamnatocin nahiyar Afirka da dama sun mayar da takardar samun izinin shiga kasashensu wato Visa a matsayin hanyar samun kudin shiga, wanda suke fargabar soke shirin ta hanyar shiga tsarin zirga-zirgar mutane da fasaha da kayayyaki ba tare da shamaki ba ka iya haifar musu da gibi a kudin shiga da haraji. Domin samun nasarar shirin AU ta kaddamar da zauren tattaunawa tsakanin kasashen nahiyar, inda aka gudanar da zaman farko a Ghana kuma za a ci gaba da taba-alli sannu a hankali a sauran kasashe.