1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Ruwanda: Ya makomar wadanda M23 ta mayar?

June 4, 2025

'Yan tawayen AFC-M23 da ke rike da yanki mafi girma na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun mayar da wasu mutane Ruwanda wadanda suka ce, suna zaune a wannan yanki ne ba bisa ka'ida ba.

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | 'Yan Tawaye | M23 | Ruwanda
'Yan tawayen M23 dai, sun kwace iko da yankuna da dama a Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Hugh Kinsella Cunningham/Getty Images

Duk da dai cewa hukumomin Ruwanda sun yi maraba da su amma da dama daga cinkinsu sun ce an mayar da su gida ne ba tare da son ransu ba, lamarin da ya saba da dokokin kasa da kasa. Ruwanda ta bude cibiyoyi a kan iyakarta, domin karbar 'yan gudun hijirarta da ake taso keyarsu daga makwabciyar kasa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Bayan mayar da su a kan ajiye su tsawon makwanni a wata cibiya da ke Mutobo a gundumar Musanze, inda ake horas da su tare da cusa musu akidar son kasa. Kana idan za a yaye su hukumomin kan ba su jari, domin bude sabon babin rayuwa a Ruwanda. An samar da wannan tsari ne, a karkashin wata yarjejeniya da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Ruwanda da kuma Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR.

Karin Bayani: Felix Tshisekedi ya dora wa Joseph Kabila karar tsana

Sai dai a watan Mayun da ya gabata, 'yan tawayen M23 sun cafke fararen hula fiye da 300 tare da iza keyarsu zuwa kasar Ruwanda. Yawancin iyalan na tsugune ne a sasanonin 'yan gudun hijira na Sake, kuma an hana su komawa kauyensu na asali wato Karenga a lokacin da 'yan tawayen na M23 suka kwace Goma babban birnin Kivu ta Arewa. 'Yan tawayen sun kafa hujjar cewa mutanen 'yan asalin wani yanki ne na Ruwanda, inda har yanzu da akwai sauran birbidin kungiyar 'yan tawayen Hutu ta FDLR mai adawa da fadar mulki ta Kigali. Sai dai a mahangar Bram Verelst mai bincike a cibiyar nazari kan sha'anin tsaro, 'yan tawayen na M23 na yin wannan aika-aika ne da boyayyiyar manufa da nufin cika wasu burukan Shugaba Paul Kagame.

Dalilan da ke sa rikicin gabashin Kwango ci gaba da kamari

03:21

This browser does not support the video element.

Har yauzu dai babu sahihan alkaluman yawan 'yan gudun hijirar Ruwanda da ke tsugune a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, saboda an gaza yi musu rijista. Sai dai an kiyasta cewa yawansu ya kai kusan dubu 200, to amma kididdigar karshe da aka gudanar a shekara ta 2018 ta nunar da cewa mutune dubu 75 ne kadai. Rayuwar wasu daga cikin 'yan gudun hijirar ta saje da ta al'ummar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon kuma ba sa sha'awar komawa Ruwanda, yayin da wasu kuma ke tsoron shiga komar kotu ko kuma bita da kulli daga mahukuntan Kigali bayan sun koma gida.

Karin Bayani: Ilimi ya tabarbare sakamakon rikici a gabashin Kwango

Ko ma dai me ake ciki, Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da matakan baya-bayan nan da 'yan tawayen M23 suka yi amfani da su wajen mayar da 'yan gudun hijira zuwa Ruwanda, lamarin da kakakin Hukumar Eujin Byun ta ce ya saba wa dokokin kasa da kasa. Batun mayar da 'yan gudun hijirar Ruwanda da ke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango gida ko kuma sake tsugunar da su, ba ya daga cikin batutuwan da aka tabo a tattaunawar zaman lafiya da kasashen biyu suka fara. To amma manazarta kamar Bram Verelst sun yi amanna cewa ba za a samar da mafita mai dorewa ga dubunan 'yan gudun hijirar ba matukar fadar mulki ta Kigali ta tsaya kan bakanta na dakile 'yan tawayen Tutsi na FDLR ba tare da yin la'akari da makomar wadannan iyalai ba.