1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 14 a Indiya

Abdul-raheem Hassan
February 8, 2021

Mutane 14 sun mutu wasu 170 sun bace bayan narkewar dalar kankarar da ta haddasa ambaliya a arewacin jihar Uttarakhand, masu ayyukan ceto na ci gaba da neman wadanda lamarin ya ritsa da su.

Indien Schlammlawine nach Gletscherabbruch
Hoto: Indo Tibetan Border Police/AP Photo/picture alliance

Wasu hotunan bidiyo daga yankin da kankarar ta narke ya nuna yadda ambaliyar ta karya gadoji da lalata tituna da kuma tashar wutar lantarki guda biyu.

Yanzu haka dai an ceto mutane 12 da rai a cikin wasu ramuka, yayin da ake kokarin ceto wasu mutanen kusan 30 da suka makale.

Hukumomi sun bude madatsar ruwa guda biyu domin takaita ambaliyar, an kuma gargadi mutane su guji zuwa kusa da kogunan da ke yankin.