1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Indiya da Canada sun sallami jakadun kasashen biyu

October 15, 2024

Dangantaka na kara tsami tsakanin Indiya da Canada sakamakon halaka wani 'dan gwagwarmayar addinin Sikh a kasar Canada.

Firaministan Canada Justin Trudeau da takwaransa na Indiya Narendra Modi a taron   G20 na shekara ta 2023 da aka gudanar a kasar Indiya.
Firaministan Canada Justin Trudeau da takwaransa na Indiya Narendra Modi a taron G20 na shekara ta 2023 da aka gudanar a kasar Indiya.Hoto: Sean Kilpatrick/The Canadian Press via AP/picture alliance

Canada ta zargi manyan jami'an diflomasiyyar Indiya da hannu wajen kashe 'dan gwagwarmayar na Sikh, Hardeep Singh Nijjar a kasarta, zargin da Indiya ta musanta wanda kuma ke ci gaba da haifar da tsamin dangantaka.

Karin bayani: China ta zargi 'yan Kanada da leken asiri

Ko a watan Satumbar 2023, Firaministan Canada Justin Trudeau ya ce yana da hujjoji na zargin hannun Indiya dumu-dumu wajen halaka Singh Nijjar, zargin da New Delhi ke cewa bata da hannu duk da cewa Singh Nijjar 'dan ta'adda ne. An dai halaka 'dan gwagwarmayar na Sikh a birnin Surrey da ke gundumar British Columbia a kasar Canada, kuma ya kasance daya daga cikin masu gwagwarmayar yada addinin Sikh da hukumomin Indiya suka haramta a fadin kasar baki daya.

Karin bayani: Kasar Canada ta nuna damurwata ga halin kasar Mali

Indiya na zargin Canada da bai wa 'yan Sikh damar yada addininsu a kasar, wadanda kuma ke kasancewa kashi 2% bisa 100 na al'ummar kasar ta Canada da kuma ke da wakilci a majalisar dokokin kasar.