1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

EU ta kulla yarjejeniyar kasuwanci mara shinge da Indiya

Abdul-raheem Hassan
January 27, 2026

Firaiministan Indiya Narendra Modi ya tabbatar da yarjejeniyar cinikayya da zai samar da rangwamen fito kan kayayyaki daga Turai, yarjejeniyar za ta bude kofa ga harkokin kasuwanci da zai habaka tattalin arzikin duniya.

EU-Kommissionspräsidentin von der Leyen in Indien
Hoto: dpa/picture alliance

Bayan kusan shekaru 20 na kwan-gaba kwan-baya na kokarin kammala tattaunawa, daga karshe dai an cimma yarjejeniyar cinikayya tsakanin Indiya da Kungiyar Tarayyar Turai EU, wacce za ta ba wa bangarorin biyu damar fadada kasuwanci tsakanin juna.

Yarjejeniyar ta sauya yanayin siyasa da kasuwanci kamar yadda aka daidaita manufofin bangarorin biyu, a cewar Gulshan Sachdeva, farfesa kuma shugaban Cibiyar Nazarin Turai a Jami'ar Jawaharlal Nehru ta Indiya. "Halin siyasar ba zato ba tsammani ya ba da damar matsa kaimi na kammala yarjejeniyar a yanzu," in ji Sachdeva.

Tun a shekarar 2007, EU da Indiya suka fara dasawa na cimma wannan yarjejeniyar kasuwanci marar shamaki, sai dai mamayar Rasha a Ukraine da barazanar harajin Amurka sun farfado ruhin tattaunawar cikin sauri.

Bayan da aka cimma yarjejeniyar, Indiya za ta yi rangwamen haraji kan barasa da motoci daga Tarayyar Turai zuwa kasar Indiya da zummar bude kofa ga kamfanonin kera motoci na Turai.