Madugun adawan kasar indiya ya rasa kujerarsa ta majalisa
March 25, 2023Talla
Ana dai zargin madugun adawan Rahul Gandhi da furta kalaman karya ga firaminista Narendra Modi bayan wani furici da ya yi kan wawure kudaden kasar.
Tun bayan da aka sanar da matakin na tube wa Rahul Gandhin rigarsa ta dan majalisa kafafen sadarwa a kasar ke bayyana damuwa kan makomar koma dimukuradiyyar kasar.
Ko da shi kansa madugun adawan Rahul Gandhi ya ce wannan wani mataki ne na yi masa bita da kulli da shi da masu adawa da gwamnatin Narendra Modi wace ta kuduri aniyar yin karan tsaye ga dumukudiyya.