1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Matan Indiya za su samu wakilci a majalisa

Zainab Mohammed Abubakar
September 22, 2023

Majalisar dokokin Indiya ta amince da doka mai mahimmanci wacce ta tanadi bai wa mata kashi daya bisa uku na kujerun majalisun kasa da na jihohi.

Indien | Wahlen im Bundesstaat Karnataka
Hoto: MANJUNATH KIRAN/AFP

Wannan zai kawo karshen takun saka da aka shafe shekaru 27 ana yi kan kudirin, batu da ya haifar da rashin daidaito da kai ruwa rana a tsakanin jam'iyyun siyasa.

Sai dai har yanzu da sauran rina a kaba, domin sabuwar dokar ba za ta shafi zaben kasa na badi ba. Za a fara aiwatar da ita ne a zabukan kasa na 2029 biyo bayan sabon kidayar jama'a da daidaita gundumomin jefa kuri'u bayan zaben shekara mai zuwa.

Majalisun Indiyar guda biyu ne dai suka kada kuri'un amincewa bai wa mata kyakkyawan wakilci. A shekarar 2021 ne ya kamata a gudanar da kidayar jama'a, da Indiya ta saba yi bayan shekaru 10, amma a karon farko ya samu jinkiri saboda barkewar annobar cutar corona.