Indiya: Bukatar agaji bayan ambaliya
August 19, 2018A cewar ministan harkokin noma na Indiyan Sunil Kumar za a yi amfani da jirage masu saukar ungulu wajen sauke kayan abinci ga al'ummar wannan jihar da ke cikin yanayi na tashin hankali. Ya kara da cewar wajibi ne gwamnati ta samarwa mutane kimanin miliyan guda wurin zama, wadanda ambaliyar ta wanke matsugunnansu, wadanda a yanzu haka ke samun mafaka a rumfunan wucin gadi da aka tanada.
Akwai dubban mutane da har yanzu ke makale a saman gidaje da bishiyoyi, a yayin da ake amfani da jiragen sama wajen daukar tsofaffi da yara kanana zuwa sansanonin da aka kebe. Tun daga ranar tara ga watan Agustan da muke ciki ne dai, sama da mutane 350 suka rasa rayukansu daga ambaliyar, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi babu kakkautawa a jihar ta Kerala, inda a halin hanzu lamura suka tsaya cik.