1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Indiya ta fara kutsa kai a nahiyar Afirka

Tijani LawalMay 27, 2011

Ƙasar Indiya na koyi da China wajen ƙarfafa haɗin kai da ƙasashen Afirka da kuma kyautata ma'amallar tattalin arziƙi da ƙasashen nahiyar

A wannan makon dai jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran nahiyarmu ta Afirka, kama daga taron tattalin arziƙi tsakanin Afirka da Indiya zuwa ga taron ƙolin ƙasashen G8 da suka fi ci gaban arziƙin masana'antu a duniya da dangantakarsu da Afirka da kuma rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a yankin Abyei na ƙasar Sudan. Da farko dai zamu fara ne da jaridar Fanrfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta ce Indiya na farautar ɗanyyun kayayyaki da neman goyan baya a nahiyar Afirka. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Indiya tayi alƙawarin ba da rancen kuɗi na dala miliyan dubu biyar don ayyukan raya ƙasa ga nahiyar Afirka. Amma fa wannan hoɓɓasa da ƙasar ta Indiya ke ƙoƙarin yi ba kome ba ne illa neman yin koyi da ƙasar China. Indiya na fatan samun ɗanyyun kayayyaki a nahiyar Afirka da kuma neman goyan baya daga ƙasashen nahiyar a ƙoƙarinta na neman dawwamammiyar kujera a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya."

A wannan makon ne dai ƙasashen G8 da suka fi ci gaban masana'antu a duniya suka gudanar da taron ƙolinsu a Deauville ta Faransa. Jaridar Neues Deutschland ta yi bitar dangantakar ƙasashen da na nahiyar Afirka tana mai cewar:

"An daɗe dai ana gayyatar shuagabannin Afirka domin halartar zauren taron ƙolin ƙasashen G8, amma fa wanzuwarsu a zauren taron ba ta zarce ta ɗaukar hoto da liyafar cin abinci ba. Ba a ɗauki ƙasashen na Afirka tamkar wasu tsayayyun abokan hulɗa da za a yi kafaɗa-da-kafaɗa da su ba. Ta la'akari da haka shuagabannin da aka gayyata a wannan karon ma ba zasu sa ran samun wani sakamako na a zo a gani a game da makomar ƙasashensu daga zauren taron ba."

Al'amura sai daɗa rincaɓewa suke yi dangane da fashin jiragen ruwa a tekun baharmaliya. Bisa ga ra'ayin jaridar kasuwanci ta Handelsblatt zama ɗan fashin jiragen ruwa tamkar wani abin alfahari ne kuma wata muhimmiyar kafa ta kuɗancewa a cikin ƙiftawa da Bisimilla a ƙasar Somaliya. Domin kuwa a halin da ake ciki yanzu tuni fashin jiragen ruwan ya zama wata tsayayyar sana'a mai samar da ƙazamar riba kuma lamarin zai daɗa yin tsamari matsawar da ba a samu bakin zaren wareware shi ba, in ji jaridar ta Handelsblatt.

Ainihin gwagwarmayar ɗora hannu akan arziƙin mai shi ne musabbabin rikicin da ake famar yi a yankin Abyei na ƙasar Sudan kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta rawaito ta kuma ƙara da cewar:

"Yankin Abyei ya fi kowane haɗari a tsakanin yankunan da ake fama da rikici a cikinsu a ƙasar Sudan. Yankin ba ma kawai yana da arziƙin man fetir ba ne, kazalika kowane daga cikin rukunonin yankin da ba su ga maciji da juna na iƙirarin neman kare kansa ne daga abokan gaba. A dai halin da ake ciki yanzun ba wanda ya san yadda makomar yankin zata kasance."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Mohammed Nasiru Awal