Indiya ta fito fili ta zargi Pakistan da hannu a harin ranar 11 ga watan yuli
September 30, 2006Talla
Watanni 2 da rabi bayan harin bama-bamai da aka kan jiragen kasa a birnin Mumbai, shugaban ´yan sandan birnin ya fito fili ya zargi hukumar leken asirin Pakistan ISI da taimakawa ´yan tawayen Islama wajen shirya kai wannan hari kan Indiya. Shgaban ´yan sandan A.N. Roy ya ce wata shaida da suke da ita ta nunar da alaka tsakanin hukumar ta ISI da kungiyar Lashkar-e-Taiba mai mazauni a Pakistan da kuma wata kungiyar daliban India da aka haramta ayyukanta. Roy ya ce an jigilar bama-baman zuwa Indiya a cikin tukanen dafa shinkafa. A martanin da ta mayar Pakistan ta kira wannan zargin da cewa ba shi da tushe bare makama. Hare haren na ranar 11 ga watan yuli sun yi sanadiyar mutuwar mutane 186 yayin da wasu daruruwa suka jikata.