Indiya ta Kaddamar da rigakafin corona
January 16, 2021Talla
Kasar Indiya mai yawan al'umma biliyan 1,3 ta soma gudanar da allurar rigakafin Corona a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar yawan yaduwar cutar, kana kasar ko baya ga jami'an lafiya, ta ware karin mutane 150.000 da za su taimaki malaman kiwon lafiya wajen zartar da aikin rigakafin a wasu cibiyoyin allurai 700 da kasar ta tanada.
Sai dai bisa matsalolin sufurin allura daga wasu yankunan zuwa wasu, za a soma yi wa jami'an kiwon lafiya da wadanda suke tattare da hadarin kamuwa da cutar corona allurar a matakin farko, inda ake hasashen za su haura akalla mutun miliyan 30.