1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Zafi ya halaka mutane da dama a Indiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2023

Ministan lafiya na Indiya Mansukh Mandaviya ya bayyana cewa, gwamnati za ta yi aiki tukuru domin shawo kan tsananin zafin da ake fama da shi a kasar da rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Indiya | Delhi | Tsananin Zafi
Abun jika mokoshi kyauta ga masu wucewa saboda tsananin zafi a IndiyaHoto: Arun SANKAR/AFP

Yankin gabashi da arewacin Indiyan dai na fuskantar tsananin zafi da ya kai digiri 46 a ma'aunin Celsius a wannan mako, yayin da mahukunta ke bayyana cewa ya janyo asarar rayuka tare da kai wasu da dama gadon asibiti. Masana kimiyya dai sun bayyana cewa, tsananin zafin da ake fama da shi da a kullum yake karuwa a yankin kudancin Asiya, na da alaka da sauyin yanayi.