Ministan tsaron Indonesiya na murmurewa
October 11, 2019Talla
Binciken 'yan sanda ya tabbatar da mahara biyu da suka soki ministan na da alaka da kungiyar IS. Ministan tsaron Wiranto mai shekaru 72 ya gamu da wannan ibtila'i yayin da yake sauka daga motarsa.
Wannan harin ya faru ne gabannin fara wa'adin mulki na biyu na shugaba Joko Widodo. Yanzu haka ministan ya fara samun sauki a gadon asibiti.