SiyasaIndonesiya
Shugaban Indonesiya ya sauke ministar kudi
September 8, 2025
Talla
Wannan na zuwa ne, bayan zanga-zangar da aka yi ta nuna kin jinin gwamnati. Ita dai tsohuwar ministar kudin Sri Mulyani Indrawati ta kasance mai karfin fada aji, wadda ta taba zama babbar darakta a Bankin Duniya kuma ta rike mukamin ministar kudi karkashin shugabanni uku na kasar ta Indonesiya. Tuni Shugaba Prabowo Subianto ya nada masanin tattalin arziki Purbaya Yudhi Sadewa mai shekaru 61 a duniya, a matsayin sabon ministan kudin kasar ta Indonesiya.