Indonesiya: Gobara ta halaka rayuka
October 26, 2017Talla
Da yake magana kan wannan batu, Harry Kurniawan shugaban 'yan sandan birnin Tangerang inda kamfanin yake, ya ce ya zuwa yanzu dai sun gano gawarwakin mutane 46, sannan kuma su na ci gaba da neman wasu mutane 10 a wannan ma'aikata da ke da ma'aikata 103.
Gobarar dai ta tashi ne da wajejen karfe tara na safe agogon kasar, karfe biyu na dare agogon GMT a birnin na Tangerang da ke kusa da Jakarta babban birnin kasar.