1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS: Mu muka kai hari kan cocin Indonesiya

Ahmed Salisu
May 13, 2018

Kungiyar nan ta IS da ke da'awar jihadi ta ce ita ce ta kai harin kunar bakin wake a wata majami'a da ke kasar Indonesiya inda aka bada labarin rasuwar mutanen da yawansu ya kai 13.

Anschlagsserie auf Kirchen in Indonesien
Hoto: Reuters/Antara Foto/Surabaya Government

IS din ta dau alhakin kai harin ne a wani sako da fidda ta kafar watsa labaranta ta Aamag. Harin wanda aka kai shi a Surabaya, birnin na biyu mafi girma a kasar na daga cikin munanan hare-hare da aka kaiwa Kiristoci tsiraru a kasar. Jami'an tsaro da ke cigaba da gudanar da bincike kan harin sun ce wanda suka kai shi iyalan wani mutum ne cikinsu kuwa har matasa da yara kanana.