1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Fargabar INEC kan zaben 2023

Uwais Abubakar Idris LMJ
October 19, 2022

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriya INEC, ta bayyana cewa ayyukan kafofin sada zumunta na zamani na barazana ga yunkurinta na gudanar da sahihin zabe a kasar.

Najeriya | Zabe | 2023 | INEC | Kafafen Sada Zumunta na Zamani
INEC ta gargadi masu amfani da kafafen sada zumunta kan zaben NajeriyaHoto: Imago/Westend61

Hukumar Zaben mai Zaman Kanta ta Kasa a Najeriyar, ta bayyana yadda kafofin sada zumunta na zamanin ke yada labarun karya musamman sanar da  sakamakon zabe da bana hukuma ba, a matsayin babban kalubale ga sahihin zaben da ta himmatu wajen gudanarwa a shekara ta 2023 da ke tafe. Ana dai kallon bayanan na hukumar ta INEC, a matsayin wani mataki na yin kashedi ga kafofin sada zumuntar da ke zama fadi ba a tambaye ku ba a harkar yada labarai a Najeriyar. INEC din dai ta ce ba za ta yarda da wannan ba, domin babbar barazanar da labaran na karya ke yi ga zabe. Kafofin sada zumunta dai sun kasance hantsi leka gidan kowa a Najeriyar saboda tashen da suke yi, domin a yankuna da dama da su aka dogara wajen samun bayanai. Mafi yawan wadanda suka mallaki wayar salula, na aika sakonni na kar ta kwana musamman a lokacin zabe, ta hanyar amfani da kafafen sada zumuntar.

Kokarin INEC na tabbatar da sahihin zabe a NajeriyaHoto: Yasuyoshi Chiba/AFP/Getty Images

Farfesa Jibo Ibrahim masanin kimiyyar siyasa kuma manazarci a cibiyar bunkasa dimukurdiyya ta CDD, ya ce akwai bukatar a yi taka tsan-tsan. Amma ga Aliyu Mustapha na kungiyar masu rajin kare kafofin sada zumunta, ya kamata masu hawa shafukan su yi abin da ya dace domin kaucewa tayar da fitina musamman a lokacin zabe. 'Yan siyasa da suke a tsakiyara fage a kan wannan al'amari sun dade da daga dan yatsa a kan wannan batu na yada labarun karya, abin da Farfesa Wole Soyinka ya dade da yin gargadin cewa zai iya rusa duk ci-gaban da aka samu da ma haifar da rudani domin a yanzu in aka ji labari sai an yi kokarin tantance gaskiyarsa a Najeriyar. Dakta Yunusa Tanko  shi ne jami'in yada labarai na jam'iyyar Labour Party a Najeriyar, ya ce akwai abin da ya kamata hukumar zaben ta yi domin magance matsalar. Akwai dai sauran aiki a gaba domin duk da tsawatar da ake yi mafi yawan masu amfani da shafukan sada zumunta ba su nuna sun ji karatun ba abin da ya sanya yunkurin kafa doka ta musamman a kansu, amma abin ya ci tura.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani