1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An kara wa'adin karbar katin zabe

Uwais Abubakar Idris ZMA
January 13, 2023

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta kara wa’adin lokacin karbar katin zabe da tsawon mako guda biyo bayan korafe-korafe da wahalhalu da ake fuskanta wajen karbar katunan.

Nigeria Präsidentschaftswahlen Schlange vor Wahllokal
Hoto: Getty Images/AFP/L. Tato

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta amince da kiraye-kirayen da ake yi mata na bukatar ta kara wa'adin lokacin rarraba katunan zabe da ta tsara za'a kawo kashen aikin a ranar 22 ga wannan wata na Janairu. Bisa Karin wa'adin da ta yin a mako guda a yanzu za'a kamala aikin ne a ranar 29 ga watan Janirun nan.

Nan hayaniya ce ta kaure a daya daga cikin wuraren karbar katunan jefa kuri'ar da ke Abuja inda mutanen suka yi dafifi a kokarin karbar na su katin kafin lokaci ya kure masu. Yan Najeriyar da jamiyyun siyasa sun nuna damuwarsu a kan yadda ake tafiyar da aikin tare da neman kara wa'adi domin har zuwa wannan lokaci akwai katunan sama da milyan biyar da har yanzu basu kai hannun masu shi ba.

Mata na layin kada kuri'unsuHoto: Ma'awiyya Sadiq

A yayin da ‘yan Najeriyar suka sha fama wajen rijistar da ya sanya kara wa'adi, wannan yanayi ne ke maimaita kansa wajen karbar katunan da a wasu kasashe da dama a kan yi amfani da hanyoyi daban-daban da suka hada da aikawa mutane ta adireshinsu. Barrister Manasara Umar ya bayyana cewa a bisa doka dole ne ga hukumar zaben ta tabbatara da rarraba katunan ga duk wanda ya yi rijista.

Ganin cewa har yanzu akwai tababa a kan kamala wannan aiki, amma hukumar zaben tace bisa tsarin da ta yi bai kamata a tada hanakali ba. Har ila yau ga yau ga Zainab Aminu jami'ar hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya.

Masu jiran kada kuri'unsuHoto: picture-alliance/AP/S. Alamba

A yayin da ya rage ‘yan kwanaki kafin zaben na Najeriya da za'a fara a ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, kwararu na bayyana bukatar amfani da fasahar zamani a aiyyukan hukumar zaben don shawo kan irin wannan matsala, musamman ta hanyara bullo da katin jefa kuri ta yanara gizo wanda lambobin za'a sanya don baiwa masu ilimi zabin yin haka maimakon bin hanaya guda ta karbar kati a hannu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani