INEC ta yi wa Jam'iyyar APC regista
July 31, 2013Bayan kwashe lokaci tana jan kafa, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya, ta sanar da yi wa jam'iyyar hadaka ta 'yan adawa ta APC regista. APC dai ta kunshi manyan jam'iyyun adawan Najeriya guda uku, wadda ake ganin za ta kasance babbar kalubale ga Shugaba Goodluck Jonathan da jam'iyyarsa ta PDP a zabukan da za su gudana a 2015, idan Allah ya kaimu.
Jami'in yada labaru na hukumar zaben Najeriyar Mr Nick Dazan ya bayyana cewar, sun dauki wanan mataki ne bayan da jamiyyar ta APC ta cika dukkanin kaidojin da hukumar zaben ta gindaya ga duk wata jam'iyya kafin ta kai ga samun rijista a cikin kasar.
Har zuwa yanzu dai Kungiyar African Peoples Congress na gaban kotu domin kalubalantar cewa ita ce ta fara gabatar da bukatar ayi mata rijista da wannan suna na APC a matsayin jamiyyar siyasa a Najeriyar.
Jam'iyyar adawa ta APC dai ta kunshi manyan 'yan siyasa daga arewa kamar Janar Mohammdu Buhari mai ritaya, da kuma irinsu tsohon gwamnan jihar Lagos Ahmed Bola Tinubu daga yankin kudancin Najeriya.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar