1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Inganta cinikayya tsakanin Jamus da China

May 27, 2013

'Yan kasuwar Jamus da na China sun daura aniyar bunkasa saye da sayarwa albarkacin ziyarar aikin da Firaministan China ya kai a Berlin

GettyImages 169508185 German Chancellor Angela Merkel (R) and China's Prime Minister Li Keqiang (L) shake hands upon his arrival at the chancellery in Berlin, Germany on May 26, 2013. The new premier's three-day visit to Germany, by far China's biggest European trading partner, indicates Beijing's wish to continue its special partnership with Europe's biggest economy, analysts say. AFP PHOTO / ODD ANDERSEN (Photo credit should read ODD ANDERSEN/AFP/Getty Images)
Firaministan China Li Keqiang da Angela MerkelHoto: AFP/Getty Images

Kamfanoni a nan Jamus sun bi sahun shugabar gwamnatin kasar, Angela Merkel wajen neman a cimma yarjejeniyar sulhu domin kawo karshen barazanar samun yakin kasuwanci tsakanin nahiyar Turai da kasar Sin wato China.

Shugaban kwamitin Asia-Pacific da kungiyar kampanonin Jamus ta samar, domin wakiltar bukatun yankin Asiya Peter Loesche yace, duba da yadda ake kara samun matsala tsakanin Tarayyar Turai da kuma kasar China, suna bukatar da a tatauna domin samun sulhu a tsakani.

Wannan bayani na Loescher na zuwa ne gabanin taron da za a gudanar tsakanin shugabannin 'yan kasuwar Jamus da China a birnin Berlin, tare da shugaban Kasar China Li Keqang da a yanzu haka yake ziyarar aiki a nan Jamus.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Jaafar
Edita: Mohammad Nasiru Awal