1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kasashen Nijar da Najeriya sun kara karfafa dangantaka.

Gazali Abdou Tasawa AMA
March 18, 2022

A Jamhuriyar Nijar hukumar hadin gwiwar kasashen Nijar da Najeriya ta joint Commission, ta bayyana shirye-shiryenta na saukaka harkokin zirga-zirgar jama’a da dukiyoyinsu da ma kyautata matakan tsaro.

Deutschland l Besuch des Präsidenten Mohamed Bazoum aus Niger in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Shekaru 51 kenan da suka gabata kasashen guda biyu na Nijar da Najeriya wadanda suka raba iyaka mai tsawon kilomita dubu da 500 suka girka wannan hukuma da nufin karfafa ‚yan uwantar gado da ta hada al’ummomin kasashen biyu da kuma saukaka harkokin kasuwanci da na sauran fannonin tattalin arziki a tsakaninsu. Gina hanyoyin mota tsakanin jihohi biyar na kasar Nijar wato Damagaram, Tahoua, Maradi,Diffa da kuma Dosso da suka raba iyaka da jihohin bakwai na Najeriya na Kebbi, Sakkwato, Zanfara, Borno, Katsina, Jigawa da Yobe na daga cikin matakan farko da hukumar ta jointe commission ta mayar da hankali a kai. Said ai kuma Malam Adamou Namata mataimakin shugaban hukumar ya ce a yanzu hankalinsu ya karkata ga shirin gina hanyoyin jiragen kasa tsakanin wasu yankunan kasashen biyu.

"Akwai wani shiri na gina hanyar jirgin kasa daga Kauran Namoda zuwa Sakkwato zuwa Birnin Konni har zuwa Dosso. Projet na biyu shi ne Kano Magaria Zinder, na uku Kano Dayi, Katsina Jibiya, Maradi. Duk wadannan hanyoyi na jirgin kasa tuni a Najeriya aka shinfida su. To ga zancen da nike muku a yanzu, ta Kano-Dayi-Katsina -Jibiya-Maradi, ita an dauki matakai na fara ta da gaggawa. Najeriya ta ware kudi kamar biliyan biyu na Dalar Amirka. Yanzu shirye-shiryen gyaran takardu kadai ne ya tsaida aiki, amma in sha Allahu ana fara shi."

Karin Bayani :Tsaro ya gagara a Najeriya da Nijar

Sai dai wani abin da ya jima yana ci wa al’ummomin kasashen biyu na Nijar da Najeriya tuwo a kwarya da kawo cikas ga harkokin kasuwanci tsak anin kasashen biyu, shi ne na rashin samun zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tsakanin kasashen biyu. To amma hukumar ta joint commission Niger Nigeria ta ce wannan matsala ita ma ta kusa zama tarihi a yanzu.

Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

"Akwai kamfanin na (OVER LAND) wanda shi har ya kawo jami’insa y aje nan a Nijar saboda shirin wannan. Sun ce insha Allahu cikin wannan shekara ta 2022 za su soma aiki. Akwai kuma kamfanin Air PEACE wanda shit uni ya soma aiki.11 ga wannan wata na maris ya yi sawunsa na farko a nan Yamai. Ni da ministan sufuri muka tarbe shi a filin jirgin sama na Yamai. Sun ce a kowane mako za su zo sau uku. Za su taso daga Abuja, su yada zango a Kano kana su iso Yamai."

Wani batun na dabam-da hukumar hadin gwiwar kasashen biyu ta dage a kai a halin yanzu shi ne na aiki kafada da kafada tsakanin hukumomin biyu wajen yakar matsalar tsaro. Malam Adamou namata ya ce ko baya ga matakin hadin gwiwa na farauta ‘yan ta’adda tsakanin jihohin kasashen biyu, sun kuma dauki matakai na katse hanyoyin sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da tsageru masu fashin daji da satar mutane domin neman kudin fansa tsakanin kasashen biyu 

Karin Bayani : Halin da ilimi ke ciki a Najeriya da Nijar

"Wani lokacin jihohin Zamfara da Sakkwato suka dauki matakin katse wayar salula saboda ‘yan ta’adda suna saduwa da juna. Da ya zo mu nan Nijar ba mu dauki mataki ba, sai kawai ‘yan ta’addan su ketaro nan Nijar kan iyaka su saye layukan Nijar su ci gaba da aiki. To amma a yanzu mun yi wata yarjejeniya ta daukar mataki na bay daya a duk lokacin da matsalar ta taso sai mu katse layuka a kasashen biyu a lokaci daya ."

A karkashin tsarin Wannan hukuma ta jointe commision Niger Nigeria wacce cibiyarta na a birnin yamai na Jamhuriyar Nijar, dan Najeriya ne ke rike da mukamin shugabancinta a yayin da dan nijar ke zama mataimakinsa. Kuma hukumar ta kunshi jami’ai daga kasashen biyu wadanda ake kallo a matsayin 'yan tagwaye.