Ingantuwar Dangantakar Jamus da China
October 11, 2012![](https://static.dw.com/image/16297497_800.webp)
Talla
Bayan ganawarsa da takwaransa na China, Yang Jiechi harkokin wajen Jamus,Guido Westerwelle ya ce hakan na zaman wata gagarumar nasara ga kasashensu biyu duk da kuwa banbance-banbace da ake samu sakaninsu. Westerwelle ya jadadda bukatar bin hanyoyin limana domin warware takaddamar da ke tsakanin China da Japan da kuma sauran kasashe makwabta da ke a wannan nahiya akan wasu tsibirai da ke cikin tekun gabashin China. Babbar manufar wannan ziyara ita ce samar da hadin gwiwar aikin soji tsakanin Jamus da China.Maaikatar harkokin wajen Jamus ta ce Westerwelle zai kuma yi magana game da bukatar kare hakkin bil Adama a kasar ta China.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu