Ingila ta kai wasan karshen na kasashen Turai
July 11, 2024Ingila ta kai wasan karshe na neman cin kofin kasashen Turai. Ingila ta samu nasara kasar Netehrlands da ci 2 da 1, lokacin fafata a wasan jiya Laraba a birnin Dortmund na yammacin Jamus a wasan kusa da na karshe. Ita dai kasar da Jamus take daukan nauyi wannan gasa mai tasiri.
Karin Bayani: Aski ya zo gaban goshi a gasar Euro 2024
Ranar Lahadi mai zuwa ake kammala wasan inda za a tantance kasar da za ta lashe wannan kofi tsakanin Spaniya da Ingila. Ita dai Spaniya ta kai wasan karshen bayan doke Faransa da ci 2 da 1 a wasan kusa da na karshe. Kuma yanzu tsakanin Spaniya da Ingila za a tantance kasar da za ta lashe wannan kofi na Turai.
A can ma yankin Amirka, Ranar Litinin mai zuwa za a kara wasan karshen na cin kofin nahiyar na Copa tsakanin kasashen Ajentina da Kwalambiya. Ita dai Ajentian ta kai wasan karshen bayan Kanada 2 da nema a wasan kusa da na karshe, sannan ita kuwa Kwalambiya ta doke Uruguay da mai ban haushi.