1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ingila ta doke Iran a kofin duniya

November 22, 2022

Tawagar 'yan wasan Ingila ta fara gasar cin kofin duniya da kafar dama a fafatawar da ta yi a babbar gasar kwallon kafa ta duniya da ke gudana yanzu haka a kasar Katar.

Fußball-WM Katar 2022 | England v Iran
Hoto: FADEL SENNA/AFP

'Yan wasan na Ingila dai sun lallasa kasar Iran da ci 6-2. Matasan 'yan wasa irinsu Jude Bellingham da Bukayo Saka ne suka sanya Ingila yin wannan bajinta a wasanta na farko a gasar da ya gudana a ranar Litinin da daddare.

Kyaftin din tawagar 'yan wasan Ingila Harry Kane bai sanya alamar kyaftin mai launin kalar goyon bayan 'yan madigo da luwadi kamar yadda aka yi hasashen zai yi ba a gabanin wasan. Hakan ta biyo bayan janye yunkurin sanya wannan alama da tawagogin kwallon kafa na Ingila da Jamus da sauran wasu kasashen Turai suka yi biyo bayan takaddamar da ta faru tun bayan da hukumomin Katar masu bin addinin Islama suka bukaci duk wanda ya halarci gasar kwallon kafar ta duniya da ya mutunta al'adunsu a yayin zamansa a kasar.