1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IOC ya ce ba zai binciki Infantino ba

July 24, 2026

Matakin ya biyo bayan zargin da aka yi wa Infantino na aikata ba daidai ba a gasar Kofin Duniya ta 2026.

Matakin ya biyo bayan zargin da aka yi wa Infantino na aikata ba daidai ba a gasar Kofin Duniya ta 2026
Matakin ya biyo bayan zargin da aka yi wa Infantino na aikata ba daidai ba a gasar Kofin Duniya ta 2026Hoto: Takuya Yoshino/AP Photo/picture alliance

Kwamitin Wasannin Olympics na Duniya (IOC) ya ce ba zai binciki zargin da ake yi wa shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya Gianni Infantino ba.

Kwamitin ya fadi haka ne bayan da aka zargi Infantino da karya dokokin hukumar tare da mu'amalarsa da shugaban Amurka, Donald Trump.

FIFA ta ce Iran za ta je gasar cin kofin duniya ta Amurka

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta FairSquare ta sanar a farkon wannan watan cewa ta shigar da kara ga IOC kan Infantino.

Karar ta yi nuni da matakin da FIFA ta dauka na dakatar da aiwatar da hukuncin dakatar da ɗan wasan gaban Amurka, Folarin Balogun, daga buga gasar Kofin Duniya, bayan da Shugaba Trump ya bukaci Infantino da kansa ya sake duba jan katin da aka bai wa dan wasan.

FIFA: Infantino zai mutunta matakin bincike

Ko da yake Infantino mamba ne na IOC, kakakin kwamitin ya bayyana cewa kwamitin ya yanke hukuncin cewa ba shi da ikon binciken lamarin, domin karar ta shafi yadda FIFA ke gudanar da harkokinta da yanke shawara, ba dangantakarta da IOC ba.