1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IPC: Yunwa ta barke a wani yankin Gaza

August 22, 2025

A karon farko an tabbatar da yunwa ta barke a yankin Gaza Governorate, yankin da birnin Gaza ke cikinsa tun daga ranar 15 ga watan Agusta.

Hoto: AFP/Getty Images

Wannan na kunshe ne a rahoton da kungiyar kula da ingancin abinci ta duniya, wato Integrated Food Security Phase Classification (IPC), ta fitar a wannan Juma’a tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.

Karin bayani: Kwararru sun yi gargadi kan halin matsananciyar yunwa da Zirin Gaza ke ciki

Kungiyar ta ce bayan watanni 22 na rikici maras yankewa, sama da mutane 500,000 a Gaza na fuskantar matsananciyar yunwa da talauci da mace-mace. An kiyasta cewa yara kanana kusan dubu 132 masu kasa da shekaru biyar za su shiga cikin rashin abinci mai gina jiki nan da zuwa watan Yunin 2026,  adadi wanda ya ninka sau biyu daga hasashen da aka yi a watan Mayu.

Sai dai ma'aikatar harkokin waje ta Isra'ila ta yi watsi da wannan rahoto, tana mai cewa "babu yunwa a Gaza.” Haka zalika, hukumar COGAT mallakin Isra'ila  mai kula da harkokin Falasdinawa, ta ce rahoton bai da tushe kuma ba ya nuna gaskiyar abin da ke faruwa a kasa.