Kanu ya bukaci kotun Najeriya ta wanke shi
January 19, 2022![Karte Nigeria Biafra](https://static.dw.com/image/5126411_800.webp)
Jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB mai rajin ballewa daga Najeriya Nnamdi Kanu ya musanta sabbin laifuka takwas da gwamnatin Najeriya ke zargin shi da aikatawa a zaman kotun da aka yi a wannan Laraba.
A cikin makon nan ne dai gwamnatin Najeriya ta kara sabbin laifukan, cikinsu kuwa har da zargin Kanu da ta'addanci da tunzura jama'a. Galibin zarge-zargen na da alaka da kalaman na Kanu wanda ke da takardar zama dan kasar Burtaniya ya yi a shekara ta 2018 a gidan rediyonsa mai suna Radio Biafra.
Sai dai kotun da ke Abuja ta dage ci gaba da shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Fabrairu, a yayin da kotun za ta ci gaba da nazarin lauyoyin Kanu na cewa a yi watsi da zarge-zargen da gwamnati ke masa.
A gefe guda wata kotu da ke jihar Abia a kudancin Najeriya ta umurci gwamnatin kasar da ta biya Nnamdi Kanu Naira miliyan dubu daya, a matsayin diyya saboda samamen da jami’an tsaro suka kai gidan mahaifinsa cikin watan Satumbar 2017.