1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

IPOB na ci gaba da tilasta wa al'umma zaman gida

Muhammad Bello RGB
June 5, 2023

'Yan kungiyar IPOB sun ci gaba da aiki da tsarinsu na tilasta wa jama'ar kudu maso gabashin Najeriya zaman gida, duk da cewa gwamnatoci na hana jama'a yin biyayya ga kungiyar.

Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu
Jagoran Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Tun a watan Agustan 2021 ne, kungiyar mai rajin kafa kasar Biafra wato IPOB ta bullo da tsarin tilasta wa jama'ar yankin kudu maso gabashin Najeriyar zaman gida, inda ta zabi ranar Litinin a duk mako don tabbatar da hakan. Hakan na zaman wani mataki ne da IPOB ta dauka don kokarin tilasta wa gwamnatin Najeriya ta sako musu jagororansu Nnamdi Kanu wanda har yau har gobe ke tsare. Kanu na fuskantar shari'a kan zarge-zarge da dama da suka hada da cin amanar kasa.

Tun dai bayan fara zaman dirshan din kimanin shekaru biyu yanzu, ko da ya ke jama'ar yankin kan mara bayan takidin na IPOB, sai dai wasu a yankin ba sa son hakan,tare da tunanin cewar zaman dirshan din na takura rayuwarsu tare da kassara tattalin arzikin yankin.

A wannan Litinin din, bayanai sun tabbatar cewar, jama'ar yankin sun bi umarnin na IPOB na kin fitowa musamman ma jahar Enugu da gwamnan jahar ya yi kurarin sa kafar wando daya da duk wani ma'aikacin gwamnati da ya bi umarnin na IPOB.

Yanzu ta bayyana karara, in ban da jahar ta Ebonyi, daukacin ragowar jahohin Anambra da Imo da Abia da kuma Enugu da gwamna ya yi kurarin sa kafar wando daya da IPOB din, umarnin ba zai daina aiki ba nan kusa.

Rayuka da dama gami da dukiyoyi ba adadi sun salwanta a yankin na Igbo a dalilin tilasta wannan zaman dirshen na gida, inda za a ga 'yan kungiyar ta IPOB na sintiri a rana mai kamar ta yau don sa kafar wando daya da ma su kunnen kashi da umarninsu a daukacin yankin in ban da jihar Ebonyi.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani